<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>544</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yau muna da murna, muna godiya
 Ga Allah Uba domin wannan rana
 25 ga watan 12, shekara kuma ta 96
 Ranar da masu bi duka suka keɓe
 Don tunawa da haifuwar Issa Almaihu.

[V2]
 KORUS
 Yau...dukan masu bi, suna yin murna
 Yau...a duniay duka, suna yin murna
 Yau...cikin Afirka, suna yin murna
 Yau...cikin (ƙasa), suna yin murna
 Yau...cikin (gari), suna yin murna
 Yau...cikin (ekklisiya), suna yin murna
 Yau...mala'iku ma, suna yin murna (2x)
 M-m-m-m-m-m, muna yin murna
 Ha-ha-ha-ha-le-lu-yah, muna yin murna.

[V3]
 2) Yau an haifa mana Issa Almasihu
 Ɗan Maɗaukaki, ya zo duniya nan.
 Budurwar Maryamu ce, fa ta haife shi.
 Jibra'ilu ne, ya shaida sunansa.
 Haifuwarsa kuma, abin al'ajabi ce.
 Girma da ɗaukaka nasa ne har abada.

[V4]
 KORUS
 Is-sa Ɗan Maryamu?...I, Ɗan Maryamu.
 Is-sa Kalmatulahi...I, Kalmatulahi.
 Is-sa Ruhunlahi...I, Ruhunlahi
 Is-sa Mai Cetonmun...I, Mai Cetonmu
 M-m-m-m-m-m, muna yin murna
 Ha-ha-ha-ha-le-lu-yah, muna yin murna.

[V5]
 Daga #45
 Karatu na 1: Yohana 3:16
 &quot;Gama Allah ya yi ƙaunar duniya, har ya bada ɗansa haifafe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi, kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.&quot;

[V6]
 Karatu na 2: Yohana ta 1 5:12
 &quot;Wanda yake da Ɗan, yana da rai,
 Wanda ba ya da Ɗan Allah, bai da Rai&quot;</lyrics>
<title>Waƙar Noël : Yau Muna da Murna LW544</title>
</song>